Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukubar Rayuwa Da Shahararriyar Mawakiya Whitney Houston Ta Sha


Wani fim da aka yi kan rayuwar Shaharariyar mawakiyar nan da ta rasu Whitney Houston, ya nuna cewa bata ji dadin rayuwa kamar yadda ake tunani ba. Zakin muryar ta ya sa ta yi suna a harkar waka a duniya, amma rayuwar ta abar tausayi ce wadda take cike da matsaloli da dayawa da suka yi sanadiyyar sata rungumar shaye shaye.

Duba da yadda ‘yan uwanta suka nemi su tatike ta da yawan ta basu kudi da abin duniya tare da iko da yadda take gudanar da rayuwar ta, da sa ido da aka yi mata kan ko wakokin ta sun fi gamsar da mutane fararen fata, tare da yawan yi mata tambayoyi kan zamantakewar ta na zama cikin auren ukuba.

Abinda fim din ke kara dubi a kai shine yadda dan uwan ta shima mawaki da ake kira Dee Dee Warwick yayi ta mata fyade yayin da take karama, da ake wa wata kawar iyalan Houston tambayoyi kan rayuwar Whitney, tana yarinya, sai ta ce babu wani abin aibu ko matsala a rayuwar Whitney tana ‘yar yarinya.

Wata ‘yar uwar Whitney, ta bayana cewa ta san cewa an yi wa ‘yar uwar ta fyade tana yarinya, ta ce “idan muna maganar sai ta kalle ni ta ce min Mary, nima anyi min Fyade, Amma ba namiji bane, ma ce ce tayi min fyade, takan yi kuka tana mai cewa mahaifiyar mu bata san ukubar da muka fuskanta ba, amma mahafiyar Whitney takan tambayi yar uwar ta cewa ko na yi wani abin kuskure ne da ya sa ake neman diya ta da lallata? Nakan amsa ta da cewa ba haka bane”.

Wani fim da ta fito a ciki The Bodygaurd ya haifar mata da matsala tsakanin ta da mijin ta Bobby Brown, ganin yadda matar sa ke ta samun nasara tana cigaba hakan ya sanya shi cikin kunci a shekarar 1993 wanda ya sa aka daina ganin sa.

A iya cewa Bobby na kishin nasarar matarsa ne kawai a tunanin sa na da namiji bakin fata, ya za ‘a yi a ce hakan ya kasance. ta so su cigaba da zaman aurensu hakan ya sa ta dan janye daga bayanar jama’a dominn ya ya cigaba da kasancewa gaba da ita. Houston sai ta nemi mijin ta Bobby Rown ya zama shine manajan ta don bashi muhimmanci, amma ba’a nan zuciyar sa take ba, ya so jama’a su so shi yadda ake son ta.

‘Yan uwan Houston su suka ta fara shaye shaye har ta tsunduma ciki ta yadda zai yi mata wahala ta daina, wani dan uwan ta Michel Houston ya bayana cewa saboda yawan yadda kwakwalwar su ke daukan kayan mayen da kan hallaka mutane, su sai su sha kuma ba abin da yake yi masu. Daga karshe ya bayyana cewa Bobby karamin alhaki ne idan ana zancen shaye shayen, mu, sai mun sha mun rage muke samma Bobby.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG