Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amitabh Bachchan Ya Yi Godiya Ga Masoyansa


Shekaru 36 bayan mumunanan hantsarin da Amita Bachchan yayi lokacin da ake shirin fim din Coolie, kawo yanzu Amitabh bai manta kuma bai daina godewa waddanda suka dage da yi masa addu’ar Allah ya sa ya rayu ba.

Tauraron dan wasan ya rubutu a shafin sa na twitter cewa yana yima ilahirin wadanda suka yi ta masa addu’ar ranar zagoyowar haifuwar sa.

Tauraron dan wasan fina finan India ya ce da ba don addu’ar mutane ba da ya zama tarihi, ya ce addu’ar mutane ce ta dawo dashi daga mutuwa.

Ilahirin al’umma a fadin duniya na ta taya shi murnar cika shekaru 75 da haihuwa, Amita Bachchan, da aka fi sani da BIG B’’ ya ce bai zaci zai rayuwa ba, yace ba zai taba mantawa da mutanen da suka yi masa fatan Alheri ba, kuma bai san ta yadda zai fara biyan su ba, amma yana matukar godiya tare da yi masu fatan Alheri.

Ya kuma kara da cewa wata rana zai bada labari cikakke akan yadda hatsarin ya faru.

Mun sami labarinne daga kamfanin dillacin labarai Indian Express App.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:55 0:00

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG