Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kowanne Ɗa Da Baiwar Sa - Inji Mawakiya Khadija A K A J


Khadija Abdullahi Nuraddeen wacce aka fi sani da A K A J- mawakiyar hip hop da rap wacce ta fara waka tun tana makarantar sakandare kuma Niki Minaj ce jigon ta, kamar yadda muka tattauna da ita sabuwar mawakiya da ake tunani bata iya wakar ba taje yunkurin yi

Ko da ta fara waka kamar ragowar mawakan Kahdija ta ce bata fuskanci wata matsala ba daga wajen iyayenta ba, iyaye basu kawo mata cikas ba domin tun tasowarta ta ke daukar littafi da biro a hannunta tana rubuce-rubuce na waka sakamakon yadda take sha’awa.

A zantawar ta da wakilyar dandalinvoa, Baraka Bashir, mawakiya Khadija A KA J ta bayyana yadda take Isar da sakonni da fadakarwa ta hanyar waka duk kuwa da cewar bata jima da fara waka ba, tana wakarta ne da harshen turanci da kuma harshen Hausa.

Har yanzu dai Khadija bata kammala karatunta na boko ba, amma tana da burin karanta harkar kasuwanci koda shike a cewarta ko bayan ta kammala karatu baza ta bar waka ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:51 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG