Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Akwai Yiwuwar Hollywood Zasu Gayyaci Shah Rukh Khan Kuwa?


Duk da yake kowa ya san fittacen Jarumi Shah Rukh Khan ya dade yan fitowa a fina finan indiya wato Bollywood Kuma ya shirya fina finai ba iyaka. Jarumin yayi korafin cewa bai san meyasa kawo yanzu ba'a taba gayyatar sa ya fito a fina finan turai ba, musaman ma Hollywood na Amurka.

Yanzu haka Shah Rukh Khan na aiki kan wani sabon fim din sa mai suna ‘Zero’, wanda Aanad L Rai ya fito a ciki da zai bayyana a gidan silma a watan Dicamba mai zuwa na wannan shekarar, wanda kuma Katrina Kaif da Anushka Sharma suka fito jarumai a ciki.

A wata ganawa da aka yi da shi kwanannan, jarumin ya bayana cewa yayinda abokan aikin sa da dama suka samu shiga wajen fitowa cikin fina finan da kasashen turai ke shiryawa, shi dai har yanzu bai taba fitowa a fina finan Hollywood na Amurka ba, saboda ba’a taba gayyatar sa ba ko a bashi wannan dama.

Masu fitowa a fina finan India na Bollywood kamar su Priyanka Chopra, Irrfan Khan, Anupam Kher, Amitabh Bachan da marigayiya Om Puri, da ma wasu da dama sun samu nasarar fitowa a fina finan Hollywood, har sun samu yabo kan haka.

Amma Shah Rukh Khan, da aka fi kiran sa da SRK, ya ce shi ya fi son fina finan India su kai matakin kasuwanci na karshe da za’a iya damawa da su a fadin duniya. Jarumin ya ce bai san dalilin da ya sa har yanzu ba’a taba gayyatar sa ba, cikin raha yana mai cewa “ko dai ban iya turanci ba ne yadda ake so”.

Khan ya ce yana fatar lokaci zai zo da jaruman ‘yan fim na Hollywood kamar su Tom Cruise za su ce sun rattaba hannu kan fim din Bollywood da mai shirya fina finai kamar Christopher Nolan zai ce akwai wani a India dake son ya shirya fim din.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG