Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jarumai Goma Na Bollywood Da Suka Fi Samun Kudi


Amitabh Bachchan
Amitabh Bachchan

An fidda sunayen jaruman Bollywood goma da suka fi samu kudade shiga inda Shah Rukh Khan, ke kan gaba da dalar Amurka $38M, daga fina finan da kuma tallace tallace.

​Salman Khan, shi ke biye masa da dalar Amurka $37M, inda fim dinsa mai suna Sultan wanda ya kasance fim na biyu da yafi tasiri a Bollywood a shekarar 2016, ya taimaka masa wajan samun wanna matsayi.

Akshay Kumar, shi ke mataki na uku, da dalar Amurka $35.5 inda fina finan sa kamar Dishoom da Jolly LLB2, suka taka rawar gani da kuma tallace tallace.

Amir Khan, wanda ya zo na hudu yakan dade bai yi fim ba amma fim dinsa na Dangal ya taka rawar gani bama a kasar Indiya, kade ba har ma da kasar waje, kuma fim din har yanzu yana ci gaba da samun karbuwa a duniya.

Sauran sun hada da Hrithik Roshan, na biyar da dalar Amurka $11.5M, Deepika Padukone, na shida da dalar Amurka $11M, Ranveer Singh da Priyanka Chopra sun kasance na bakwai da $10M.

Amitabh Bachchan, shi kade ya rage a cikin tsofafafin hannu a Bollywood, da har yanzu yake jan zarensa inda yazo mataki na tara da dalar Amurka $9M sai kuma Ranbir Kapoor na goma da dalar Amurka $8.5M.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG