Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Rashin Matashin Tauraron Mawaki


Al - Amir Hassan Bello Danbatta
Al - Amir Hassan Bello Danbatta

A shirinmu na nishadi a wannan makon zamu tabo babban rashin da masana’antar Kannywood tayi ne na wani yaron mawaki na Rap da Hip-hop da karansa ya kai tsaiko a faggen waka Allah ya karbi abinsa , a yammacin ranar alhamis din da ya gabata matashi ko ma in ce yaron mai gogawa da manya ya rasu a wani hatsarin da ya rutsa da shi a kan titin Hotoro dake Kanon Nijeriya.

Al-Amir Hassan Bello Danbatta wanda aka fi sani da lil Ameer kafin rasuwarsa DandalinVOA ya tattauna da marigayin tare da abokinsa inda ya bayyana mana dalilinsa na fara waka , waiwaye dai ance adon tafiya ga hirarmu da shi da muka gudanar na wancan lokaci

A cewarsa ya fara waka ne ganin cewar, ya lura babu kananan mawaka a nan nahiyar Afrika wanda shi ya ja hankalinsa har ya fara, ya ce yana waka kuma yana karatu a lokaci daya.

Mahaifiyarsa Khadija shehu Muhammad ta bayyana sanadiyar rasuwarsa biyo bayan hatsarin inda alokacin yana kan machin sai suka yi karo da mai adaidaita sahu watau keke Napep, bayan sun fadi daga bisani sai wata mota ta hau kansa.

Ta kara dacewa ta ji labarin rasuwar marigayin ne daga sama domin ta jtyi tafiya zuwa Katsina gaisuwa daga dawowarta ,sai ta gwada lambarsa shiru, sai labarin rasuwarsa suka ji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG