Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bollywood Ta Fitar Da Wasu Fina Finai Biyu


Kangana Ranaut
Kangana Ranaut

Yau Bollywood, zata fitar da wasu fina finai biyu masu suna Simran da Lucknow Central, duk fina finan akwai alamun cewa zasu yi tasiri wajan nishadantar da masu kallo.

Farhan Akhtar, ya dawo faggen fina finai bayan da fim dinsa na baya mai suna Rock On 2, wanda bai tabuka abin arziki ba, itama jaruma Kangana Ranaut, ana sa ran cewa fim dinta mai suna Simran, zai bata damar dawowa da kwarjininta a faggen fina fina da samun ta goma shi.

Akshaye Rathi, wani mai harkar fina finai ya ce yana da kyakkyawan tabbacin cewa fina finai biyu zasu baiwa marada kunya idan har abinda suka kunsa zai yi tasiri ga jama’a.

Ya kara da cewa koda yake duk fina finan babu tabbacin cewa a tashin farko zasu samar da makudan kudade, amma hakkan zai dogara ne ga batun da mutanen da suka kalli fim din suka yi dangane da kawun fim din wanda zai sawa mutane kwadayin suma su so kallon fim din.

Ya cigaba da cewa kowane jarumi nada bukatar fim dinsa ya yi tasiri ta yadda zai baiwa marada kunya, amma a wasu lokuta ko jarumai kamar su Shah Rukh Khan, Salman Khan da Aamir Khan , suna yin fim din da bazai tabuka abin azo again ba domin ba ko da wanni lokaci miya kan yi dadi kamar yadda ake zato ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG