Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fim Din Akshay Kumar Ya Doke Na Shah Rukh Khan


 Akshay Kumar Bollywood
Akshay Kumar Bollywood

Fim din Akshay Kumar,Toilet Ek Prem Katha, ya baiwa marada kunya a Bollywood, inda fim din ya taimakawa ma’sana’abtar ta Bollywood samun makudan kudaden shiga a daidai lokacin da masana’antar ke neman fadawa kwata.

Hakan ya biyo bayan yadda fim din ya shiga zukatan jama’a, domin ya tabo rayuwar mutane kasar Indiya ne. Fim din kuma ya yiwa fim din Shah Rukh Khan, Jab Harry Met Sejal, fintinkau,

Daga dukkan ala’mu yanzu an daina kallon fim domin suna a kasar Indiya, sai dai domin sakon da fim din ke dauke dashi ga jama’a, ganin yadda fim din Akshay Kumar ya doke fim din Shah Rukh Khan, duk da sunnan da gida Khan, yayi a faggen fina finai.

A yanzu dai Ashay Kumar, na cin Karen sa babu babbaka domin kuwa tana kaimashi kuma ya kasance a yanzu jarumin da za a iya saka jari akansa ba tare da fargaba ba domin kuwa ya san yadda yake dadadawa masoyan sa rai

Abin da ya jawowa fim din Shah Rukh Khan, koma baya bai wuce labarin fim din ba wanda jama’a ke ganin cewa bai da wani tasiri sosai ga rayuwarsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG