Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bagobiri Sullutu Na Daya Daga Cikin Mawakan Hip-Hop Na Farko - Inji Hassan K-Boy


Kamar yadda muka alkawarta wa masu sauraronmu muna nan dauke da cigaba da hirar mu da mawakin rap a da wato Hassan Muhammad Auwal, ya ce al’ummar malam bahaushe bata bai wa mawakin rap gurbin da zata shiga jerin mawaka ba, in baya ga yanzu da aka fara sauraren su.

Matashin ya ce da yawa ana kallon mawakan rap- da hip-hop a matsayin marasa da’a, a sakamakon irin yanayin shigarsu ta kayan sawa da basa daga cikin al’adar Hausa.

Ya ce tarihi ma ya nuna cewa rap daga Africa ya fito inda wani mawaki "Bagobiri sullutu da matarsa yake waka matarsa tana yi masa cafiya.

Daga karshe ya ce a zamanin da aka yi cinikin bayi mafi yawan su na bayyanawa junansu damuwarsu ta hanyar waka ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:54 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG