Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Daura Auren Kawarta Jaruma Priyanka Chopra Ta Sami Matashi


Shaharariyar ‘yar wasan fim din Indiya ‘’Bollywood’’ wacce kuma takan fito a fina finan Hollywood, Priyanka Chopra, da shahararen mawaki Nick Jones, sun yi baiko ranar asabar din da ta gabata. Piryanka cikin murna da farin ciki ta hau shafin ta na Instagram inda ta dora hoton ta tare da saurayin nata, tana masa kallon soyaya a hoton tare da nuna zoben da ya sa bata.

A cewar kafar talabijin aa E! News, Saurayin nata Nick dan Shekaru 25 ya rubuta a kasan hoton da ta sanya a Instagram, yana mai cewa “Son Barka…Na fi kowane namiji sa’a a duniya”. Bayan ta dora hoton na farko a shafin nata sai ta ba masoyanta mamaki inda ta dora hotunan bikin baikon nasu da aka yi a Birnin Mumbai, a Indiya.

A cikin Hotunan, Priyanka yar shekaru 36 ta fito sanye da kayan al’adar ta mai kalar ruwan dorawa haka shima saurayin nata ya sanya kayan da maza ke sawa na alada’r kasar Indiya. Haka zalika iyayen Chopra, da Jonas’ sun bayyana a cikin hotunan da aka dauka a gaban wani guri da ake kira Golden N and P emblem.

Masoyan sun fara soyaya ne jim kadan bayan sun dawo daga auren kawar su Meghan Markle, da aka yi a Windsor, kasar Ingila ranar 19 ga watan Mayun da ya gabata. Ana yada maganganun cewa jarumar da mawakin sun yi soyayar watanni biyu ne kachal.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG