Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za'a Fafata A Gasar Firimiya Lig 2016/2017 Mako Na 19


A cigaba da wasannin firimiya lig da akeyi na 2016/2017, na kasar Ingila mako na Goma sha tara, yau za'a kece raini tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Hull City da Everton.
Wasan zai kasance da misalin karfe Tara na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi, Gobe idan Allah ya kaimu kuma Burnley za ta karbi bakuncin Sunderland, Chelsea zata kara da Stoke City, Leicester City zata kece raini da Westham, Manchester United kuwa zata kara da MiddleBrough, Southampton da Westbromwich,Swansea City zata gwabza da AFC Bournemouth.

Babban wasan da zai dau hankali a Gobe shine wasan da za'a kara tsakanin kungiyar Liverpool da Manchester City, da misalin karfe shida da rabi na yamma.
Sauran wasannin kuma za'a buga da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya Nijar da kamaru.

A ranar Lahadi kuwa, Watford zasu fafata da Tottenham, Arsenal zasu karbi bakuncin Crystal palace.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG