Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta lallasa Sunderland A Gasar Firimiya 2016/2017 Mako Na 18


A cigaba da wasannin firimiya lig shekarar 2016/2017 da ake a kasar Ingila, jiya Kungiyar kwallon kafa ta Watford tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Crystal palace

Masu rike da teburin firimiya a yanzu haka Chelsea ta doke AFC Bournemouth da kwallaye 3-0

Arsenal ta samu nasara akan Westbromwich daci 1-0

Leicester City bataji da dadiba a gidanta domin Everton ta shata 2-0

Har ila yau Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta lallasa takwararta na Sunderland da kwallaye 3-1

Swansea city, ta sha kashi a hannun Westham da ci 4-1

Yayinda itama Burnley, ta dandana kudarta a hannun MiddleBrough da ci 1-0

Hull City ba tasha da dadiba a hannun Manchester City daci 3-0

Asaman teburin kuwa har yanzu kungiyar Chelsea Ki mataki na daya da Maki 46

Manchester city na mataki na biyu da maki 39

Ita kuwa Liverpool na mataki na uku da maki 37 a wasa goma Sha bakwai da tayi da zarar ta samu Nasara ko kunnen doki a wasanta na yau zata koma mataki na biyu

A kasan teburin kuwa Sunderland tana mataki na goma Sha takwas da maki 14

Swansea na mataki na goma Sha tara da maki 12

Hull City na mataki na Ashirin itama da maki 12

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG