Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Eden Hazard Ya Jefa Kwallonsa Ta 50 A Gasar Firimiya


Sakamakon nasarar da Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta samu a gasar firimiya lig 2016/2017 mako na gama sha takwas a jiya tsakaninta da Kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth inda Chelsea tasha 3-0, dan wasanta mai suna Eden Hazard ya jefa kwallonsa cikon ta hamsin a gasar firimiya ta kasar Ingila a tun lokacin da ya fara mata wasa

Hazard ya samu damar jefa kwallonne a bugun daga kai sai mai tsaron gida (penalty) a wasan da suka yi a jiya da Bournemouth a lokacin ana minti na arba'in da tara da fara wasan

Hazard dan kasar Belgium, ya zamo mutum na shida cikin jerin "yan wasan Chelsea, da suka zurara kwallaye 50, a firimiya a lokacin suna taka leda a Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Wadannan 'yan wasa sune Frank Lampard, Didier Drogba, Jimmy Floyd. Sauran sune Hasselbaink, Gianfranco Zola da Eidur Gudjohnsen.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:36 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG