Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Leicester City Sun Nuna Bacin Ransu A Kan Ajiye Ahmed Musa A Benci


Labarin da yake fitowa daga Kungiyar kwallon kafa ta Leicester city da ke kasar Ingila, wasu daga cikin magoya Bayan kungiyar sun nuna rashin jindadinsu na ganin yadda mai horas da kungiyar Claudio Renieri, yake kin yin amfani da dan wasan gaba na Super Eagles, ta Najeriya Mai suwa Ahmed Musa, a wasu manyan wasanni da Kungiyar ta ke yi musamman a wasannin firimiya lig.

Magoya Bayan sun baiyana hakane jim kadan Bayan an tashi daga wasan da Leicester tayi da kungiyar kwallon kafa ta Everton, inda Leicester, ta sha kashi daci 2-0 a hannun Everton a ranar litinin data wuce a gasar firimiya lig mako na takwas.

Jama’ar sun rubuta a shafukansu na sada zumunta na yanar gizo cewa idan baza'a yi amfani da dan wasanba to a barshi ya koma tsohon kulob dinsa na CSKA Moscow dake kasar Rasha.

Ahmed Musa shine dan wasa na biyu mafi tsada a kungiyar ta Leicester City, ya je kungiyar ne a farkon kakar wasan bana daga Kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow, akan kudi Fam miliyan £16.

Leicester ce take rike da kambun firimiya lig na shekarar 2015/2016 inda a yanzu haka take mataki na goma sha shida a gasar firimiya lig ta 2016/2017.

A jiya kuma kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Stoke City da ci 4-1. A cikin wasannin yau kuwa kungiyar Southampton, zasu kara da Tottenham a gasar firimiya 2016/2017, mako na goma sha takwas

Za'a buga wasan da misalin karfe tara Saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

XS
SM
MD
LG