Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Ce Tunda Akwai 'Yan Wasa Irinsu Messi Tilas Ya Jira


 Lionel Messi
Lionel Messi

Dan wasan gaba na kasar Brazil mai taka leda a Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, mai suna Neymar yace yana jin dadin zama a kungiyarsa ta Barcelona, a yanzu .

Neymar mai shekaru ashirin da hudu da haihuwa ya ce burinsa shine yaga ya zamo zakaran kwallon kafa na duniya, yace amma ba dole ba sai dai yace zai yi kokari iya kokari a doka tamola.
Ya kara da cewa tunda akwai manyan ‘yan wasa irin su Lionel Messi, sai dai ya jirasu domin komai lokacine.
Yana mai cewa shi dai ya dauki wasan kwallon kafa a matsayin sana'a, ne kuma ta kasance abinda sha'awa gareshi.

Neymar, na mataki na biyar a cikin jerin sunayin gwarzayen kwallon kafa na duniya na shekarar 2016, Wanda akayi a cikin wannan watan Disamba 2017.

XS
SM
MD
LG