Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mata Ta Auri Bishiya Mai Shekaru 100


A jihar Florida dake kasar Amurka, wata mata ta dauki alwashin kare tsohuwar bishiyar da take kauna wacce ta wuce karni guda sakamakon yunkurin sare bishiyar da aka yi. Saboda haka, kawai ta auri Bishiyar kamar yadda kafafen yada labarai a Florida suka rawaito.

An daura auren matar mai suna Cooper da Jibgegiyar bishiyar wacce take kafe a filin shakatawa na Snell Family Park, dake Fort Myers inda aka watsa furanni yayin bikin, gami da dan karamin kare da ya riko zoben, Kai har da Cake na daurin aure gami da kwalliya da ake yi a wuraren bukukuwan aure.

Cooper, ta ci kwalliya da rigar da amare ke sanyawa yayin daurin auren su inda ta saka farar riga ta silki mai adon leshi, masu kallo kimanin Hamsin ne suka halarci wannan daurin aure wanda aka yi alkawarin auren akan idanuwansu, An ayyana sare bishiyar ne sakamakon wani da yake son sayen wurin amma yake kokwanton kin saye sai in har zai sare bishiyar saboda bazai iya biyan inshorar ta ba in hadari ya afku, bishiyar ta fado akan wani ko wata.

Jibgegiyar bishiyar na tsakiyar filin shakatawa amma wani bangare na inuwar rassan ta mai fadin sikwaya 8000 ya fada akan filin da yake mallakar wani.

Maganar sare bishiyar mai shekaru fiye da dari na fita makwabtan da ke zaune a kusa da wurin suka fara kamfe da zanga zangar kin nuna goyon bayan sare bishiyar wanda sanadiyar haka wannan mata ta auri bishiyar.

Cooper, ta fadawa manema labarai cewa ta sami kwarin gwiwar yin hakan ne bayan samun labaran mata da suka rika auren bishiyoyi a kasar Mexico a matsayin zanga zangar nuna rashin goyon bayan kan sare bishiyoyi da ake yi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG