Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Kwallo A Amurka Sun Nuna Rashin Jin Dadin Su Kan Kisan Wani Matashi Bakar Fata


‘Yan kungiyar wasan kwallon kafar Amurka NBA da ake kira Boston Celtics da Sacramento Kings sun hadu jiya Lahadi don nuna rashin ajin dadinsu akan kisan wani ba-Amurke bakar fata mara makami da ‘yan sanda suka yi.

‘Yan wasan sun sanya riguna da aka rubuta “A tabbatar da gaskiya, dukan mu daya muke” a gaban rigar sai kuma sunan marigayin a bayan rigar wato “#StephonClark.

Ranar 18 ga watan Maris ne Clark ya rasu a kudancin Sacramento. ‘Yan sanda sun zarge shi da balle motocin jama’a, kuma lokacin da jami’an tsaron suka tunkare shi, sun harbe shi har sau 20 bisa tunanin yana dauke da bindiga. Sai daga baya aka gene cewa waya ce kawai ke hannun sa.

Magajin garin Sacramento, Darrell Steinberg yayi kira akan a gudanar da cikakken bincike akan abinda ya faru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG