Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Sami Karuwa A Gidan Ajiye Namun Daji Na Kasa A Washington DC


Lokacin da Baraka ya ga Calaya take jinin su ya hadu, kuma anga yadda suke shakatawa kasan jinin su ya hadu a lokacin da suka hadu gidan adana namun daji na birnin Washington DC.

Yanzu haka Calaya 'yar shekaru 15 Gwaggon birinya daga nahiyar Afirka da yanzu haka ke gidan ajiye dabbobi na kasa Smithsonian na gab da samun karuwa d'a ko 'ya ta fari. wato Baraka zai sami magaji na farko da ya rayu.

Ma’aikatan gandun adana namun daji da kuma al’ummar da ke da ra’ayin kula da Birrai sun matsu domin ganin wannan rana da za’a haifi Gwaggon biri, domin kuwa ba’a ga irin wannan lamarin ba tun tsawon shekaru tara da suka gabata.

Melba Brown, matar da ke kula da kuma koyar da Calaya, ta fada a yau alhamis cewa “cikin birinyar ya tsufa kwarai” kafin nan an auna cikin da duba lafiyar Jaririn, inda ta kara da cewa gab Calaya take da haihuwa.

Birran guda biyu kamar yadda mujallar Washington Post ta wallafa, sun kasance cikin soyayya tun daga ranar da aka kai Calaya gidan ajiye namun dajin shekaru uku da suka wuce. Akwai Birai jinsin Gorilla ko gwaggo, guda shida a gidan ajiye dabbobin na kasa.

Shi dai Baraka, yana da shekaru Ashirin da biyar, da akai wa lakabi da Silver Back a turance sakamakon gashi mai tarin yawa dake bayansa, wanda nauyinsa ya kai Pound 425 kwatankwacin Kilogram 192 kuma shine Oga kwata kwata na birran dake gidan, domin kuwa shike shiga tsakani yayin da rikici ya barke a tsakanin Biran da kuma baiwa kowa lokacin kwanciya bacci.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG