Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daya Daga Cikin Dalilan Masu Zuwa Yawon Bude Ido Indonesia Shi ne Al'adunsu


Masu zuwa yawon bude ido a kasar Indonesia sun karu a cikin shekarar da ta gabata soboda yadda aka tallata kasar a kasashen ketare da kuma gine ginen zamani da aka yi. Shugaba Joko Widodo ya ce zai gina wuraren bude ido guda 10 kamar yadda aka tsara tsibirin Bali.

Babu tantama, Indonesia kasa ce mai kyau, kuma gwamnatin kasar na so ta fadawa duniya hakan. Yadda aka tallata kyawun kasar ya taimaka wajen kara yawan masu yawon baki dake zuwa yawon bude ido zuwa miliyan 14 a shekarar da ta gabata, kusan karin kashi 22.

Amma wannan cigaban na cike da kalubale, don masu sukar lamiri na ganin hadarin cigaban da ya wuce kima a kasar.

Yanzu haka a tsibirin Benoa dake Bali, masunta na fada akan mallakar wani fili don gina kasaitaccen wurin shakatawa.

Gwamnatin kasar na fatan yawan masu zuwa ziyarar yawon bude ido zai kai miliyan 17 a cikin shekarar nan kuma a cewar ma’aikatar yawon bude ido, yawancin bakin dake zuwa kasar na zuwa ne don ganin al’adu da albarkatun kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG