Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tela ko Likitan Dabbobi Ina Zata Kaya


Sana'ar Matasa
Sana'ar Matasa

‘Ya’ya na bukatar goyon bayan iyayen su dan cimma burin su a rayuwa, karmar Zainab Ibrahim Adamu, wata daliba ‘yar makarantar sakandare kuma mai koyon dinki wanda aka fi sani da Tela.

Zainab, dai ‘yar shekaru goma sha ukku, wace tace ta bukaci iyayen ta dasu bata damar goyon aikin dinki suka ko goya mata bayan yin haka.

Da take ganawa da wakiliyar muryar Amurka, Baraka Bashir, ita dai Zainab, tace burinta shine ta zama Likitan dabbobi, dan tana da sha’awar ganin cewa a kowane lokaci dabbobi na cikin lafiya da walwala.

Ta kara da cewa dinkin da take yin a yanzu bazai hanata cimma burinta na zama Likitan dabbobi ba domin tana samun goyon bayan iyayenta.

XS
SM
MD
LG