Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Van Gaal Yace David de Gea Ba Zai Kama Kwallo Ma United Jumma'ar Nan Ba


Louis van Gaal ya ci gaba da tsayawa kan bakarsa game da batun sayen dan wasa Pedro, yayin da ya sake tabbatar da cewa David de Gea ba zai kama musu kwallo a karawar da Manchester United zata yi da Aston Villa jumma'ar nan ba.

Dan wasan gaba na Barcelona Pedro yana shirin barin kulob din a bayan darektan wasanni na Barcelona, Robert Fernandez ya tabbatar cikin wannan makon cewa dan wasan mai shekaru 27 da haihuwa yana son barin kulob din.

An yi ta yayata rade-radin cewa Pedro zai koma Manchester United, amma manaja van Gaal yace su a wurinsu, "dan wasan gaba na farko shi ne (Wayne) Rooney, na biyu kuma shi ne Chicarito (Javier Hernandez). Tsarinmu ke nan, in akwai hanyar da zamu kara karfin kulob din zamu yi."

Ya ci gaba da cewa, "Na sha fada cewa zamu sayi karin dan wasa ne kawai idan muka ga yin hakan zai taimakawa tsarin da muke da shi."

Har ila yau, van Gaal ya ce mai tsaron gida Sergio Romero shi ne zai kama kwallo ma Manchester United a karawar da zata yi jumma'ar nan da Aston Villa a wasan lig na Firimiya, yayin da ake ganin cewa de Gea na hanyar barin kulob din zuwa Real Madrid.

Kafin wasan farko na kakar kwallo ta bana, manajan na Manchester United kuma dan kasar Netherlands, ya bayyana cewa mai tsaron gida de Gea ba ya cikin halin da zai iya kama musu kwallo.

XS
SM
MD
LG