Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari ya Bada Watani Ukku a Kassara Boko Haram


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta bullo da sabon salo wajen fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram, bayan umurnin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba ta jiya Alhamis, cewa ta kassara kungiyar mai tsattsauran ra'ayin addinin cikin watanni ukku masu zuwa.

Mukaddashin jami'in yada labarai na Ma'aikatar Tsaron Najeriya Kanar Rabe Abubakar, shi ne ya yi wannan bayanin, bayan da Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin manyan jami'an soji jiya Alhamis a Abuja.

Sabbin manyan jami'an sojin sun hada da Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya; da Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai, Hafsan Sojin Dakarun Kasa na Najeriya; da Vice Admiral Ibok-ete Ekwe Ibas, Hafsan Sojin Dakarun Ruwa; da Air Marshal Sadiq Abubakar, Hafsan Sojin Dakarun Sojin Sama.

Kanar Abubakar ya ce a shirye sojojin su ke su kara kaimi don ragargaza Boko Haram.

XS
SM
MD
LG