Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil ta Dawo da Ricardo Kaka Domin ya Murza Mata Leda


Ricardo Kaka
Ricardo Kaka

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Orlando City, Ricardo kaka, ya bayana cewa Alhamis din nan ta kasance babban ranar gareshi saboda dawo dashi da aka yi dan ya bugawa kasar sa wato Brazil ta maula gabanin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za’a buga a shekarar 2018, a kasar Rasha.

Dan shekaru 33, dan wasan gaba kuma wanda ya jefawa kungiyar sa ta Orlando City, kwallaye har tara a raga, abunda ya taimaka aka sa sunan sa a cikin ayarin wadanda zasu buga wasan sada zumunta tsakanin Brazil, da kasashen Costa Rica da Amurka, a wata mai zuwa.

Kaka, a yanzu haka shine na biyu wajen jefawa Orlando City, kwallaye a raga a kakar wasa na bana, kuma ya kasance dan kwallon da yafi kowa murza leda a wasan su da Tottenham.

Kaka ya murzawa Brazil, leda a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, a shekarun 2002, 2006 da kuma 2010.

Wasan da ya bugawa Brazil, na karshe shine wanda suka yi da kasar Japan a shekarar bara wato 2014, inda suka lallasa Japan, da cin 4, da nema. A wasani 89, daya bugawa Brazil, ya jefa mata kwallaye 29, a raga.

XS
SM
MD
LG