Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Falcons ba Haka Aka so ba


Kwallon mata
Kwallon mata

A Ci gaba da kasar cin kofin kwallon kafa na Mata na duniya, Amurka ta doke Najeriya, da ci daya mai banhaushi a wasan da suka buga a Vancouver, ta kasar Canada.

Koda yake ‘yan Super Falcons, din sun taka leda yadda yakamata, amma babu sa’a , ana cikin ruguntsumi ne Abby Wambach ta kasar ta Amurka, tayi nasarar jefa kwallo a ragar ‘yan Super Falcons, ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.

Kungiyar ta Super Falcons, dai sau 7, take lashe gasar kofin zakarun nahiyar Afirka,

Kuma tunda aka fara gasar cin kofin kwallon kafa na mata na duniya a shekarar 1991, Najeriya bata taba fashi ba.

A gasar ta bana Najeriya ta fara ne da yin kunnen doki 3 da 3, da kasar, Sweden, sailin nan kuma sai kasar Australia, ta doke ta da cin 2, da nema.

XS
SM
MD
LG