Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Samartaka Da Harshe A Kasar Hausa


Nigeria Feast and Fear
Nigeria Feast and Fear

A cikin shirin Dandalin VOA na Harshe da Samarta taka zamu cigaba ne akan rarrabuwar Karin magana a harshen Hausa, zakuji tattaunawar Dandali da samari da 'yan mata kan wa yafi rikon alkawari a fannin soyayya.

Dr. Abdullahi Garba Imam, malami ne a kwalejin Aminu Kano (legal studies) ya yi bayani akan rabe-raben karin magana, Inda yace akwai Karin magana mai kamanceceniya, akwai mai mutuntawa, akwai mai aibuntawa, akwai Mai dabbantawa, akwai kuma mai kwarantawa. Missali, kamar karin magana Mai dabbantawa itace wadda za a dauki wasu kalmomi wadanda mutum aka sani yana amfani da su, amma sai a dauka a ba dabba a cikin Karin maganar, wanda sai aga kamar dabbar ce ke magana.

Missali, kamar a ce Allah wadan naka ya lalace, wai rakumin dawa ya ga na gida. Wani missalin kuma shine; ban ga dama ba, wai ance kare ya bada waka. Haka kuma Karin maganarki da ta ce, in gani a kas, wai ance Ana buki a gidan su kare.

A fannin samartaka kuma, dandalin VOA ya zanta da matasa akan tsakanin mata da maza wa ya fi rikon alkawari a fannin soyayya. Wata matashiya da ba ta fadi sunanta ba tace in har mace na son namiji tsakani da Allah, ba za ta kula wani ba sai shi. Ta kara da cewa mata na da alkawali sosai muddin suna son mutum.

Duk da cewa wasu na gani mata ba sa so tsakani da Allah, matashiyar tace ba duka aka taru aka zama daya ba. Amma dai ta shaida cewa masu irin wannan son, da rikon alkawalin basu da yawa.

A nasa bayanin kuma, malam Abdul'aziz cewa yayi, mata sun if maza kishi. Don in mace na sonka, a duk fadin duniya ba ta da wani sai Kai. Ya Kara da cewa su mata yarda ce matsalarsu, amma in har da yarda, da kuma tabbas akan son da mace ke yi to lallai zata iya bijirewa iyayenta. Bayan haka, zata iya zama da kai a duk yanayin da kake ciki.

A cikin mata an sami wasu da suka rasa rayukansu saboda so. Amma da wuya a sami hakan a bangaren maza. A cewar malam Abdul'aziz. Ga Baraka Bashir da Karin bayani.

XS
SM
MD
LG