Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Banga Bata Matasa Bace - Inji Maraya Fagge


“Yadda siyasa ke tafiya yanzu, abin ya zama tamkar kasuwar biyan bukatun wasu tsiraru ne, domin manyan ‘yan siyasa na siyasar son zuci da kuma abinda za’a samu,” a cewar wani matashi mai suna malam Suleman Maraya Fagge.

Suleiman ya ce a yanzu siyasa babu bin ra’ayi, duk matashin da ke bin abinda uban gidansa ke yi, suna bin son zuciyarsu ne kamar yadda iyayen gidan keyi. Ya kara da cewa wani lokacin jahilci na taka rawa a siyasar matasa.

Matashin na ganin cewar matasa da yawa na siyasar jahilci, da zarar sun sami ‘yan canji shi kenan, ba su damu da manufar dan takararsu ba.

“Akwai bukatar matasa su fahimci cewar jagororinsu ba sune a gabansu ba. Ya kamata su dinga maida hankali akan cancantar dan takara, don tabbatar da cewa mutun ne da ya san abinda ya keyi,” a cewar Suleiman.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG