Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Azumi Daga Kasar Amurka


Watan Azumi na daya daga cikin watanni da musulamai ako ina a fadin duniya ke jiran zuwan shi, kasancewar ibadar da ake yi a cikin watan ga duk musulami zai kauracema cin abinci daga fitowar rana har zuwa faduwarta, lokaci ne na ibada da neman kusanci da Allah.

Wata ne da iyalai kan hadu don cin abincin budabaki da bukukuwan sallah a karshen watan, Inas El Ayouby, dake zaune a birnin Vienna dake jihar Virginia ta kasar Amurka, ta bayyana yadda shirye shiryen azumin ke gudana a garin nasu.

Sukan kawatar da gidajen su, da sababbin kayan sawa kayan kwanoni da kofufukan cin abinci, haka gidan zai dinga wani sabon kamshi saboda shine wata mai albarka. Sai ta kara da cewar “Mukan ji matukar dadi a wannan lokacin domin kuwa yadda muke kayatar da gidajen mu yana bayyana muhimancin wannan lokacin, kuma mukan rungumi juna da kyautatama juna a cikin watan”

Kayatar da gidajen da suke yi yakan koyama yara cewar wannan wani lokaci mai matukar muhimanci a rayuwar musulmai, duk da cewar yaran basu kai shekarun azumi ba, duk dai da cewar takan kawatar da gidanta a duk lokacin wani buki, ganin cewar tayi sabo da hakan tun a kasar su ta Masar.

Sai ta kara da cewar takan samu kayan kawatar da gidanta wanda ake kawo mata daga kasar Masar, wasu kuma takan samesu a nan kasar, mutane da kanyi wannan sana’ar sukan samu makudan kudade don samar da kayan kawatar da gida musamman a wannan wata mai rahama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG