Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Fadakar Da Matasa Illar Bangar Siyasa - Inji Dan Zaki


Idris Dan Zaki
Idris Dan Zaki

Idris Dan Zaki Burum-burum mawakin siyasa ne a fannonin da suka danganci yanayin siyasa, a cewarsa domin fadakar da al’umma dangane da dabi'unsu da akidunsu a harka ta siyasa da irin abubuwa da suka kamata al’umma ta yi la’akari da su a lokacin yakin zabe.

Ya ce yawancin wakokinsa na siyasa na fadakarwa ne tare da sanar da matasa muhimmancin kaucewa bangar siyasa kamar yadda wasu matasan ke yi a fagen siyasa, wadanna na daga cikin batutuwa da wakokinsa ke mayar da hankali akai.

Dan Zaki ya ce yana nuna illar amfani da kudi wajen sawo hankali mutane a fagen siyasa domin samun kuri’u da ‘yan siyasa kan yi amfani da ci domin cimma muradansu- inda yake fadakar da wannan sakon domin kaucewa wadannan ‘yan siyasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG