Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baahubali 2 Ya Fi Kowane Fim Kasuwar Tikiti A China


Gobe Asabar za a saki film din Baahubali na 2 a kasar China bayan yayi suna a kasuwannin India, film din da Shetty da Prabhas suka fito a matsayin taurari a ciki, yanzu haka dai film din yafi kowane film sayar da tikiti wanda ya kasance sai ma mutum ya nemi a ajiye masa kafin ya samu ya saya, ana sa ran sai yafi kowane fim sayar da tikiti a China.

Duk da harsashen cewa film din yayi fice amma abin mamaki shine har yanzu Baahubali bai kai matsayin film din Bajrangi Bhaijan na Salman Khan ba.

Draman Kabir Khan, wanda ya nuna a gidajen kallo 8000, a China a watanin baya da suka wuce, yayin da aka saki film din SS na rajamouli Magnum a gidajen kallo 7000.

Baahubali na 2 ya nuna tauraron ‘yan wasan film din India Rana Daggubati, Tamannah Bhatia, Ramya Krishnan, Sathyaraj da Nassar, a cikin film din. an kuma nuna film din da harshen yaren Hindi wanda ya samu ribar kudi har rupee 511, a lokacikn da ake nunawa masu nazari kafin a sake shi ga Al’umma baki daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG