Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fim Din Superhero Ya Yi Farin Jini A Indiya Tun Kafin Ya Fito


A yau ne kanfanin fim din Avenger: Infinity War, ya fitar da sanarwar gagarumar nasarar da ya samu ta sayar da tikitin shiga kallon sabon fim din sa da jama’a ke dakon jira, mai suna “superhero”.

kamfanin ya bayyana cewa sama da mutane miliyan daya ne suka sayi tikitin shiga kalon sabon fim din da za a fitar kwana kwanan nan.

Kwararru sun bayyana cewa kawo yanzu, shine fim na biyu da ya samu karbuwa da farin jini bayan fim din Baahubali, kum har yanzu jama’a na ci gaba da sayen tikitin.

Daga karshe kwararru sun bayyana cewa wannan fim zai kasance daya daga cikin manya manayan fina finan Hollywood da ya sami karbuwa da farin jini a kasar Indiya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG