Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamar Sana'a Kan Iya Zama Ta Kasa-da-Kasa


Amina Umar Saulawa
Amina Umar Saulawa

Amina Umar Saulawa – tana sana’ar kayan da suka shafi dangin kayan mata, sana’a ce mai bukatar hakuri da juriya domin harka ce da ake mu’amala da mata daban daban, duba da yanayi da ake ciki a yanzu.

Ta ce ta fara sana’ar ne don kauda al’adar nan ta mata ta bani-bani wanda ke sa a kosa da mace ko a gundura da ita, bayyana cewa ta fara sana’ar da kadan-kadan wato ta fara ne da sayar da kayan kitchen na mata a wancan lokaci.

Sannu a hankali sana’ar ta fara habaka inda aka dinga shigo da wasu kayan, sabanin na kitchen zuwa kayayyakin yara da na manya, sannu a hankali aka gangaro zuwa kayan kujeru da gadaje. Ya zuwa yanzu bata fuskanta matsala daga wajen masu saye da sayarwa, sa'annan bata fuskantar kalubale wajen shigo da kayayyakin daga kasashen wajen, a cewarta don tana bin dukkanin ka’idojin da aka gindaya na shigar da kaya daga wata kasa.

Amina, ta ja hankali mata da su tashi tsaye tare da jajircewar ba sai an jira miji ko dan uwa ba kafin a zamo masu dogaro da kai, ta ce rashin raina sana’a shi ke kawo cigaba da dinbim albarka a tattare da harkar kasuwanci.

Ta kammala da cewar da sannu ake cimma dukkanin muradu da dan Adam kan sanya a gabansa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG