Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kaddamar Da Manhajar Hana Nacewa Wayar Hannu Mai Amfani Da Kudi


Katafaren kanfanin fasahar nan na Google, ya bada sanarwar kirkiro da wata sabuwar manhaja da zata taimakawa mutane rage yawan nacewa amfani da wayar hannu a koda yaushe a Burtaniya.

Kamfanin ya bayyana cewa manhajar zata ba mai amfani da wayar damar saita ta da kuma yadda yake so ta yi masa aiki. Ita dai wannan manhaja zata yi aiki ne kamar haka; mai waya zai saita manhajar da akwatin ajiyar sa na banki wato Bank Account a turance.

Misali, idan mai amfani da waya na bukatar daina amfani da wayar sa ko kaurace mata na wani lokaci, sai a saita da ta yadda idan lokacin bai kai ba, da zarar mai wayar ya bude ta zata dauki adadin kudin da mutum ya saita ta ba kungiyoyin bada agaji.

Wannan zai kasace tamkar wata hanya ce ta hora mai amfani da wayar da kuma tunasar da shi cewar a duk lokacin da yake bukatar kaurace ma wayar, ya zama wajibi ya kiyaye kokuma aljihun sa ya yi kuka.

Mun samo wannan labara ne a mujallar Telegph.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG