Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai An Ba Mata Dama Sa'annan Za'a Iya Tantance Gazawar Su


Ana yi wa matan arewa matasa kallon marasa hazaka a wuraren ayyuka mussamam ma kasancewarsu mata inji Amina Zubairu Yahya, wata matashiya da ta ce tana fuskantar kalubalen kasancewarta mace kuma ma’aikaciya .

Ta ce ba a wajen aiki kadai ba hakan ya samo asaline tun daga karatunta na jam’ia inda ta fara fuskantar kalubale da dama, matashiyar ta kara da cewa a yayin da ta nemi karantar ilimin sanin albarkatun kasa bata samu ba sai aka bata kwas din harshen Turanci wato English, kuma fuskanci wasu matsaloli a matsayinta na daliba da wasu malamai.

Da farko dai ta ce matsalar da ta samu it ace, wani malaminta ya nuna yana sonta, rashin amince masa ya kasance mata da tangarda, sa’annan bayan kammala karatunta kuma, ta samu aiki amma sai ta lura jama’a na yi mata kallon gazawa wanda aganinta tamkar take hakkin mata ne.

Daga karshe Amina ta bayyana sai al’umma ta ba mata dama sannan za’a iya tantance gazawarsu da akasin haka, duk kuwa da cewar akwai wasu lokutan da mace ke da rauni

Ga cikakkiyar hirar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG