Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kasashe Da Su Kafi Kudi A Fadin Duniya!


Kudin Kasashen Duniya
Kudin Kasashen Duniya

A wani bincike da aka gudanar da ya bayyanar da kasashe ashirin da biyar 25, da sukafi kudi a duniya, da yadda kasashen suka samu kudaden su. Muna tafe da jerin wadannan kasashen. Kasar farko itace kasar “Qatar” wadda take cikin daular kasashen larabawa. Kasar dai nada karfin tattalin arziki, dake bayyanar da kwatankwacin kudin, da kowane dan kasar yake samu a shekara.

A kasar dai da keda yawan mutane 2,172,065. Mutane kan samu albashi daya kai dallar Amurka $139,760 dai-dai da naira 30,952,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na tsawon shekaru 79, kamun mutuwa.

Baki daya a shekarar 201 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $211.8 Billiyan. Dai-dai naira tiriliyan arba’in da uku, karfin kudin su daga albarka mai ne wanda suke na 9, a duniya da sukafi kowace kasa yawa wajen ajiye mai.

Sai kasa ta biyu mai karfin arziki a duniya, itace kasar “Macao Sar, China” Kasar dai nada karfin tattalin arziki, dake bayyanar da kwatankwacin kudin da kowane dan kasar yake samu a shekara.

A kasar dai da keda yawan mutane 577,914. Mutane kansamu albashi, daya kai dallar Amurka $118,110 dai-dai da naira milliyan ashirin da hudu a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na tsawon shekaru 80, kamun mutuwa.

Baki daya a shekarar 2016 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $55.5 Billiyan. Dai-dai da naira tirilliyan goma sha daya. Karfin kudin su daga ca-ca ne, inda garin ya zama babban birnin ca-ca a yankin kasashen Asia.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG