Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

3sc Fc Bauchi zasu kece raini da Hasla Fc a Bauchi PFA Cup 2017 (Quarter final)


3sc Fc Bauchi
3sc Fc Bauchi

A ci gaba da wasannin da akeyi a cikin garin jihar Bauchi tarayyar Najeriya a gasar cin kofin da kungiya mai fafutukar ciyar da harkar kwallon kafa a jihar Bauchi Progressive Football Association, suka saka mai taken Bauchi PFA Cup 2017 1st Edition.

A yau Kungiyar kwallon kafa ta 3sc Fc dake cikin garin Bauchi zata kece raini da takwararta ta Hasla Fc, itama ta garin Bauchi a wasan dab da nakusa da na karshe Quarter Final, kuma za'a buga wasanne a filin wasa na Games Village, dake Bauchi, da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya da Nijar.

Gobe kuwa kungiyar kwallon kafa ta Samba Gwabba, zasu kara da Horse Power, suma a matakin wasan Quarter final, da misalin karfe hudu na yammaci a Games Village.

Haka kuma a jiya ne kungiyar kwallon kafa ta Red Army, dake Bauchi, ta samu nasarar zama a mataki na ukku a gasar cin kofin tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, Alh Aminu Mai gari na ‘yan kasa da shekaru ashirin 2017, Red Army ta doke Jahun Ataka.

A yanzu haka dai kungiyoyi guda biyu ke jiran wasan karshe kungiyoyin sune Samba IBB Bauchi da United Boys.

Ana sa ran za'a buga wasan karshe nan bada dadewaba inda manya manyan baki na cikin gida da waje da kuma manajojin kwallon kafa a fadin tarayyan Najeriya zasu halarci wasan domin zakulo hazikan yanwasa daga cikin Kungiyoyin don ciyar dasu gaba ta hanyar kaisu manya manyan kulob.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG