Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Zamo ‘Yar kallo A Gasar Copa Del Rey 2016/2017


A ci gaba da wasannin da akeyi na Copa del rey a kasar Spain na shekarar 2016/2017, a matakin wasan nakusa da nakusa da na karshe (Quarter Final) a jiya Kungiyar kwallon kafa ta celta vigo, tayi canjaras 2 da 2 tsakaninta da Real Madrid, a karawarsu ta biyu.

Haka kuma a a haduwarsu ta farko Celta Vigo, ta doke Real, da kwallaye 2-0 a gidan Real wanda hakan ya bada dama ga Kungiyar ta Celta vigo, zuwa wasan zagaye na kusa da karshe (Semi Final) ita kuma Real Madrid ta zamo yar kallo.

Itama Eibar tabi sahun Real Madrid, na ficewa daga gasar Sakamakon canjaras 2 da 2 da sukayi da Atletico Madrid. Atletico ta samu Nasara akan Eibar a wasansu na farko a gida daci 3-0.

A yanzu haka kungiyoyi guda ukku ne suka samu nasarar hayewa zagayen kusa da karshe Kungiyoyin sune Kamar haka, Kungiyar kwallon kafa ta Alaves da Atletico Madrid, sai kuma kungiyar Celta Vigo.

A yau kuma za'a kara tsakanin Barcelona da Real Sociedad, da misalin karfe tara da kwata na dare agogon Najeriya domin samun wanda zata shiga cikin jerin Kungiyoyin ukun don su zame cikon na hudu kafin a fafata a matakin Wasan kusa da na karshe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG