Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CINIKAYYA : Valencia Ta Jera Sahu Da Manchester Don Sayen Tsohon Dan Wsan Arsenal Da Chelsea,


A cigaba da saye da sayarwa da akeyi na ‘yan wasan kwallon kafa a duniya, Arda Turan na Barcelona yaki amincewa da komawa wata kungiyar kwallon kafa a kasar China.

Turan mai shekaru ashirin da tara da haihuwa yace yana jin dadin zamansa a kungiyarsa ta Barcelona, duk da rashin samun kansa a wasanni da bayayi a kungiyar.

PSG da Chelsea, sun shiga sahu wajan zawarcin dan wasan baya na Wolfsburg, Mai suna Ricardo Rodriguez.

Valencia, ta jera sahu da Manchester United, don ganin ta sayi tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea, Lassana Diarra dan shekaru talatin da daya da haihuwa wanda a yanzu yake kungiyar Marseilles.

Kungiyoyin kwallon kafa har guda ukku masu buga Super League, na kasar China sun nuna sha'awarsu ta ganin sun sayo dan wasan Juventus, mai suna Dani Alves, dan shekaru talatin da ukku da haihuwa.

Inter Milan, ta bukaci Kungiyar Arsenal, da ta bata dan wasanta Alexis Sanchez, ita kuma zata ba Arsenal Ivan Perisic.

Ita kuma kungiyar ta Arsenal na yunkurin kawo dan wasa mai suna Miralem Pjanic, don ya maye gurbin Alexis Sanchez in har ya koma Kingiyar kwallon kafa ta Juventus.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG