Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ware Wa Lionel Messi Fam Miliyan 100


Lionel Messi
Lionel Messi

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, a cigaba da saye da sayarwa da akeyi na ‘yan wasan kwallon kafa a fadin duniya a yanzu haka Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £100 domin sayen Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona mai suna Lionel Messi.

Itama Manchester United, ta saka fam miliyan £100 domin zawarcin dan wasan gaba na kasar Faransa Wanda yake kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, watau Antoine Griezmann.

Barcelona da Atletico Madrid, Sun sahu daya wajan zawarcin danvwasan gaba na Chelsea Diego Costa.

Hull City na neman Emenike daga kungiyar Kwallon kafa ta Fenerbahce, Arsenal da Manchester United, sun shiga neman dan wasan gaba na Westham United Dimitri Payet, MiddleBrough na yunkurin sayen dan wasan Stoke City mai suna Bojan.

XS
SM
MD
LG