Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaruma Kareena Kapoor Khan Ta Samu Ta Gomashi A Bollywood


Kareena Kapoor
Kareena Kapoor

A wannan makon a shirin mu na Bollywood, mun waiwayi jaruma Kareena Kapoor Khan, ce wace mahaifinta Randhir Kapoor, shima ya kasance fitattcen jarumi a Bollywood.

Tun baya fitowarta a wani fim mai suna war film Refugee, kareena, ta kafa kanta a fina finan Indiya, inda ta fito a wani fim din tarihi Asoka da Melodrama duk a shekarar 2001.

Bayan wannan nasarar da ta samu a wadannan fina finai sai ta samu ‘yar koma baya a shekarun da suka biyo baya. Amma shekarar 2004, ya kasance shekarar da bazata manta ba saboda fina finan da ta fito a cikinsu sun kasance mabudin alheri domin ta samu ta goma shi dalilin wadannan fina finai.

Fina finan sun hada da Chameli, wanda ta fto a matsayin karuwa, ashekarar 2006, ta sami lashe jaruman da tayi fice, a shekarar 2007, shima ta lashe kyautar wace ta kasance ta biyu a jarumai sakamakon bajintar da ta nuna a wani fim na soyayya kuma na barkwanci.

Kareena, ta ci gaba da samu nasara a faggen fina finai a Bollywood, inda ta fito a matsayin jaruma a wasu fina finai hudu.

Kareena, tana da aure, mata a gida Saif Ali Khan, rayuwarta ta kasance na sanin yakamata da kuma tsayawa akan abinda ta sani cewa shine daidai, sai kuma rawar data taka a faggen fina finai a Bollywood, kuma a yanzu haka tana da wani kamfani na sayarda kayan sawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

XS
SM
MD
LG