Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Waje Road Da Ivory Coast A Gasar AFCON 2017


A yayin da aka gwabza a fagen kwallon kafa na cin kofin nahiyar kasashen Afirka AFCON 2017 a kasar Gabon, a matakin wasannin rukuni
A jiya Kungiyar kwallon kafa ta kasar Morocco, ta doke masu rike da kambun kofin kasar Ivory Coast daci 1-0
Togo tasha kashi a hannun RD Congo da kwallaye 3-1

Inda a rukunin na (C) kasar RD Congo da Morroco suka samu hayewa zagayen nakusa da nakusa da na karshe (Quarter Final)
RD Congo ta kare da maki 7 a mataki na daya Morroco ta kare a mataki na biyu da maki 6
Ita kuwa kasar Ivory Coast da take rike da kambun gasar tayi waje rot a matsayi na uku da maki 2 kacal a wasanni uku da ta buga
Kasar Togo ta bi sahun Ivory Coast da maki 1 a wasanni uku inda ta kare a matsayi na hudu

A yau kuma za'a fafata a rukunin (D)
Tsakanin kasar Egypt da Ghana
Ita kuwa kasar Uganda zata kece rainine da kasar Mali da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya Nijar da kasar kamaru

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG