Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Celta Vigo Zata Fafata Da Real Madrid A Copa Del Rey 2016/2017(Quarter Final)


A cigaba da fafatawa da akeyi a wasannin Copa del rey 2016/2017, a matakin wasan nakusa da nakusa da na karshe (Quarter final) a Jiya Kungiyar kwallon kafa ta Alaves tayi canjaras 0-0 tsakaninta da Alcorcon a karo na biyu.

Hakan yaba Alaves damar zuwa wasan kusa da karshe wato (Semi Final) inda a haduwarsu ta farko Kungiyar ta Alaves ta doke Alcorcon da kwallaye 2-0

A yau kuma za'a kece raini a gasar Copa del rey, tsakanin Eibar da Atletico Madrid da karfe bakwai da kwata na dare, Celta Vigo kuwa zata karbi bakuncin Real Madrid, da misalin karfe tara da kwata na dare agogon Najeriya da Nijar

Har ila yau Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool zata kara da Southampton a gasar (EFL)2016/2017 a matakin wasan kusa da na karshe karo na biyu da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG