Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Bincike: Amfani Da Dumin Jikin Mutun Domin Samar Da Wutar Lantarki


A wannan karni na 21, ana iya ganin yadda binciken kimiyya da fasaha ya dauki jagorancin ganowa da warware matsalolin kiwon lafiya a fadin duniya. Hakan wani abun dubawa ne, domin kuwa an fara ganin sababbin na’urori masu duba lafiyar mutun na tafida gidan ka a wurare da dama.

Da yawa wadannan na’urorin sukan gudanar da aikin gano yadda bugun zuciyar mutun ke gudana, ko hawan jini, da dai makamantan su, mafi akasarin na’urorin na amfani da batiri, ko akan yi cajin su don aiki yadda ya kamata.

Wasu jerin masana na wani aiki don fito da hanyar da za a iya samar da wutar lantarki daga jikin dan’adam, wanda suke fatar ganin yadda zufa dake fita daga jikin mutun yayin atisaye ko kuma duk wani aiki da zai fitar da gumi daga jikin mutun.

A cewar Mr. Jamie Grunlan, na jami’ar Texas A&M, jagoran binciken jikin dan’adam na samar da kimanin karfin wutar gulof 80, suna aiki tukuruwajen ganin sun samar da hanyoyin da za’a dinga amfani da jikin mutun da za’a fitar da wuta da kuma ajiye ta don amfani da zai samar da hasken lantarki ko amfani da duk wasu abubuwan amfanin yauda kullun na gidaje.

Masu binciken sun samar da wata na’ura da mutun zai makala a jikin rigar shi, wanda ta haka na’urar zata dinga tara wutan lantarki daga jikin mutun daga iska mai zafi dake fitowa daga jikin shi.

Shugaban binciken ya kara da cewar, ba wai wannan aikin zai yuwu ba, amma yaushge? Nan da shekara daya ko biyar, ya danganta da irin gudunmawar da suka samu wajen gudanar da aikin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG