Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samsung Na Shirin Bayyana Sabuwar Wayar Da Ka Iya Zarce Ta Apple


Kamfanin Samsung ya bada sanarwar yiwuwar zarce kanfanin Apple wajan ingancin fasaha a yayin da yake shirin fitar da wata sabuwar wayarsa mai murfi wato wadda ake nunkewa.

Daya daga cikin manyan shugabannin kanfanin Mr. DJ Koh, mai kula da harkokin wayar hannu a kafar talabijin ta NBC, a ranar litini ya bayyana cewa kanfanin ka iya fito da sabuwar waya irin wadda ake nunkewa a babban taron kanfanin da za a gudanar cikin watan Satumba, yayin da ake sa ran shi ma kanfanin Apple zai fito da tasa.

Shugaban bai bayyana takamaimai lokacin da wannan sabuwar waya zata shiga kasuwannin ba, koda shike a wani lokaci ya taba bayyana kaddamar da wayar cikin wannan shekarar kokuma mai zuwa.

Ana kyautata zaton idan kanfanin ya fito da wayar wadda y ace mai saukin farashi, zata iya sauya tunanin jama’a da dama dake amfani da wayar Apple.

Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da wannan waya da akai wa lakabi da Galaxy X. Amma ana kyautata zaton girmanta zai iya kaiwa kamar na dan karamin Tablet, wato girmanta zai iya na waya kadan sannan mai amfani da ita zai iya nunke ta, ya kuma bude lokacin da yake bukatar amfani da ita.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG