Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NASA Zata Bada $750,000 Tukwici Don Sarrafa Iskar CO2


Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, ta fitar da wata gasa da za’a ba duk wanda yaci nasara kudi dalar Amurka $750,000 kwatankwacin Naira Milliyan dari biyu da saba’in N270,000,000.

Gasar dai ita ce yadda mutun zai nemo hanyar da za’a sarrafa iskar “carbon dioxide” a turance, wato iskar da mutane ke shaka, ta yadda za’a iya amfani da ita a duniyar Mars.

Gasar da aka kira “CO2 Conversion Challenge” masana kimiyya na hukumar sun bayyana cewar suna neman taimakon masana a ko ina a fadin duniya wajen cimma nasarar warware wannan matsala.

Samun hanyoyin da za a sarrafa iskar da mutane ke shaka a iya amfani da ita a duniyar wata zai taimaka matuta wajen aiwatar da wasu ayyuka a duniyar da masu bincike suke kokarin gudanarwa.

Masanan ba zasu iya gudanar da aikin su a duniyar ba, balle har suyo guzuri don zuwa duniyar da akema lakani da Red Planet. Hukumar ta bayyana cewar rayuwa a wata duniya babban abu ne, kuma bazata iya samar da duk abin da za’a bukata a duniyar ba.

Hakan yasa muke bukatar mutane masu hazaka su zo don gudanar da aikin tare da zummar samo hanyar da mutane zasu iya rayuwa a duniya ba tare da wata matsala ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG