Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samsung Galaxy Note 9 Ta Bayyana


Daga karshe dai wayar Samsung Galaxy note 9, da ana dade ana dakon jira ta bayyana. Wannnan na nufin cewar duka manyan kanfanonin wayar hannun na kan turbarsu ta fitar da waoyin hannu makamantan wannan.

An inganta wayar Galaxy Note 9, da dabarun zamani da manhajoji da dama domin biyawa mai amfani da ita bukatu daban daban, kama daga tantance zanen yatsan mai wayar, da kuma alkalamin rubutu na waya da ba a taba irin sa ba domin saukaka amfani da kyammara, kiran waya da sauran su.

Akwai rade radin cewa wannan zai iya kasancewa karon karshe da kanfanin Samsung zai fitar da irin wannan waya ta Samsung Galaxy Note 9. Ana iya samun wannan waya a manyan shagunan sayar da wayar hannu irin su Verizon, T-mobile da sauransu.

Ga kasashen dake nahiyar Afirka kuma, ba mamaki za a fara samun irin wannan waya nan ba da dadewa ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG