Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na'urar Alexa Ta Nadi Labarin Sirri Ta Kai Gaba


Wasu iyalai mazauna karamar hukumar Oregon ta jihar California a kasar Amurka, sun bayyana a wata cin ammana da na’urar Alexa ta yi masu, na’urar da mutane kan hada ta da wasu na’urorin gida kamar su talabijin, kwamfuta, na’urar sanyayya daki da dai makamantansu.

Akan hada na’urar don samun taimako a duk lokacin da mutun ya bukaci aiwatar da wani abu a gida, da ya shafi kunnawa da kashe na’urorin gidan, mutun zai umurci na’urar ta yin magana da ta yi abin da ake bukata ba tare da mutum ya sa hannu ba.

Haka mutun zai iya sanar da na’urar wasu maganganu da wani yare wanda ita kuma zata fassara zuwa harshen turanci, wani gidan radiyon KIRO 7, ya bayyana cewar an kira wata mata a makonni biyu da suka wuce wanda aka bayyana mata cewar na’urar Alexa ta dauki bayanan sirrinta ta aika ma wani dan’uwan su.

Na’urar ta bayyana asirin gidan mutane, wanda ta aika da sakon bayanin labarin da ma’auratan suka yi a tsakanin su, sun bayyana cewar hakan cin amana ne da na’urar ta yi masu, don haka ba zasu sake yadda da na’urar ta Alexa ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG