Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Twitter Zai Sa Alama Ga Labaran 'Yan-Siyasa


Kamfanin shafin sadarwa na Twitter ya bayyana sabon tsari da zai fitar wajen labarai da ‘yan siyasa ke wallafawa a shafin, a gabanin zaben tsakiya da za’a gabatar a kasar Amurka, a shekara mai zuwa.

Kamfanin ya bayyana cewar hakan zai taimaka ma mutane wajen samun bayanai masu inganci, da kuma magance matsalar satar bayanai don bude shafi da sunan wani. Tsarin zai bayyana kujerar da dan siyasa ke nema, kuma daga wace gunduma ya fito.

Alamar zata rika fitowa a duk lokacin da dan siyasa ya rubuta wani abu a shafin sa, ko kuma mutane suka mika labarin gaba, wanda a duk lokacin da labarin ya shiga cikin shafin labarai, mutane zasu gani a matsayin labari daga majiya mai tushe.

A yanzu haka dai kamfanonin sada zumunta na yanar gizo da suka hada da Twitter, Facebook da ma sauran su, suna fuskantar binciken kwakwab, daga hannun jami’an tsaro, don bari da suka yi ana amfani da shafukan nasu wajen murdiya da magudin zabe a kasashen duniya.

Sabuwar alamar zata fara bayyana kwanan nan a duk wani rubutu da ‘yan takarar gwamnoni da ‘yan majalisu na kasar Amurka su ka yi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG