Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Na Shirye-Shiryen Fara Tuki a Saudiyya


‘Yan makonni kafin mata su fara tuki karon a farko a hukumance, mata a Saudi Arabiya sun fara shirin wannan babbar rana.

Yayin da wasu ke daukar darusan koyon tuki wasu kuma sun riga sun zabi motocinsu kuma sun kagara su hau kan titi a kamar yadda wakiliyar Muryar Amurka, Mariama Diallo ta ruwaito.

Wata daya kafin lokacin da mata za su fara tuki kan titi, mata a Saudiyya sun fara gwajin iya rike sitiyari a wani wurin koya tukin mota musamman ga sabbin hannu.

Nisreem Suleiman, na daya daga cikin matan da zu sa fara tuki a Saudiyyan, ta kuma ce “ina cike da farin ciki kuma ina so in duba ire-iren motoci, da farashen su, da kuma wasu abubuwa inga abinda ya dace da ni.”

Matakin taimakawa mata wajen zirga-zirga ta hanyar ba su damar tuki abin a yaba ne a cewar wata mata ‘yar kasar ta Saudiyya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG