Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Linda Ikeji Mai Rubuce Rubuce A Shafin Yanar Gizo Ta Mayar Da Martani


Shahararriyar mai rubuce rubuce ta yanar gizo (blogging) Linda Ikeji ta nuna hotunan ta dauke da juna biyu a safin ta na sada zuminta, bayan da ta shaida tana da ciki amma jama’a sukai ta yada jita jitar cewa cikin bana gaskiya bane.

Marubuciyar ta bayyana kanta a matsayin macen da bata tarayya da maza sai kuma gashi yanzu an ganta da ciki. Toh amma ta ce a lokacin da take fadakar da ‘yan mata da su kare al’aurar su, kada su bada jikin su ga maza don kudi sai dai idon sun hadu da namijin da yake son su, su ma suna son shi amma ba wai don kudi ba.

Ta kara da cewa ita ma kanta a lokacin bata da wata alaka da namiji amma daga baya sai Allah ya hada ta da wani da yake son ta kuma suna son juna, shine dalilin da ya canza ra’ayin ta. Daga karshe ta ce baza ta bayyana masoyin nata ba a shafukan yanar gizo. mun sami wannan labari ne daga mujallar stargist.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG