Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maganin Zaman Kashe Wando


Sana'ar Dogaro da Kai
Sana'ar Dogaro da Kai

An bukaci matasa dasu tashi tsaye domin neman sana’ar dogaro da kai domin maganin zaman kashe wando.

Amina Salisu Idris, wata matashiya mai sana’ar dogaro da kai ce ta bada shawarar a zantawarsu da wakiliyar muryar Amurka Baraka Bashir, a birnin Kano.

Ta ce ta faro ne da sana’ar sayar da fashion dangogin dankunne, sarka, zube da sauran kayayyaki kyalekyale na mata don ta huce wa kai takaicin zaman duniya

ta ce Allah ne ya ce tashi in taimake ka don haka ne ta ke sana’a duk kuwa da cewar a halin yanzu tana karatu amma bai hanata yin sana’a ba.

Amina ta ce da sana’ar ne take dauke wa iyaye wasu kananan bukatu da ba sai ta tambayesu wani lokacin ma har ta dauke musu kudin mota na makaranta, idan basu bata ba.

Tana mai cewa babban burinata sana’arta, ta habbaka ta kasace itama tana daukar ma’aikata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG